Babban sakataren majalisar koli ta harkokin tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadiyyan ya tabbatar da cewa kasar Iran da Rasha zasu kara yawan musayar kayakin kasuwanci a tsakaninsu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Ahmadiyyan ya bayyana haka ne a lokacin ganawarsa da jami’i na musamman mai kula da zirga-zirgan kasuwanci tsakanin Iran da Rasha Mr Lu’iteen a nan Tehran.
Ya kuma kara da cewa hanyoyin musayar kayaki tsakanin Iran da Rasha suna da dama, akwai ta jirgin kasa mafi yawa na kayaki ne, sai motoci da jiragen ruwa da na sama.
Ya ce Iran zata fadada dukkan wadannan hanyoyi gaba daya don bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Ahmadiyyan ya yaba da inda aka kai a halin yanzu na hanyoyin musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.