Iran Ba Zata Manta Da Kissan Iraniyawa 290 Wanda Amurka Ta Yi A Shekara Ta 1988 Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran ba zata manta da kissin da sojojin ruwa na Amurka suka yi a tekun farisa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa Iran ba zata manta da kissin da sojojin ruwa na Amurka suka yi a tekun farisa a shekara 1988 ba.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Esmail Bgaei yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, a rana irin yau ce 3 ga watan Yulin shekara 1988 jirgin yakin Amurka ya cilla makamai kan fasinja Airbus A655 na kasar Iran, ya kuma kashe dukkan wadanda suke cikinsa.

Jirgin ya tashi daga Bandar Abbas na kudancin kasar Iran da nufi birnin Dubai na UAE ne amma a cikin tekun farisa, jirgin yaki Amurka mai suna USS Vincennes ya cilla makamai ya kashe mutane 290 da suke cikin jirgin, daga ciki har da yara kanana 66.

Sannan bayan wannan ta’asan gwamnatin Amurka ta lokacin tace ba zata taba neman uzuri ba, sannan banda haka ta bawa sojojin ta da suka kakkabo wannan jirgin fasinja lambobin girmamawa ta kasar Amurka ta kuma jinjina masu kan aikin da suka aikata.

Baghaei ya bayyana cewa mutanen kasar Iran ba zasu manta da wannan kissan kiyashin ba. Sannan zata bi Kadin wadanda suka aikata wannan laifin a duk inda suke a duniya daidai lokacinda ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted