Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce iran ba ta bukatar izinin kowa kan inganta sinadarin urenium din ta, don haka Amurka ta daina maganar banza da dagewa akan wannan batu inji shi.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa, babban kuskure ne a ce su (Amurka) ba za su bari Iran ta inganta sinadarin Uranium ba.
Ayatullah Khamenei ya bayyana shakkunsa game da sakamakon tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin bikin tunawa da zagayowar ranar shahadar tsohon shugaban kasar Ibrahim Raisi.
A lokacin mulkin shahid Raisi, an gudanar da shawarwari irin haka da Amurka, amma ba a kai ga cimma wani sakamako ba, inji shi, Don haka, ba ma fatan wani sakamako daga wadannan shawarwarin, kuma ba mu san abin da zai biyo baya ba.”
Ayatullah Khamenei ya yaba da irin tsayin dakan da Raisi ya yi, yana mai jaddada cewa bai taba barin makiya su iya tilastawa Iran zama kan teburin tattaunawa ta hanyar barazana, matsin lamba ko yaudara ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kuma yi karin haske dangane da dagewar da Amurka da sauran kasashe suka yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta inganta sinadarin Uranium ba.
“Tabbas, zan bayyana wa al’ummar Iran daga baya dalilin da ya sa suka dage kan batun inganta sinadarin Uranium.