Iran: An Rage Yawan Rashin Aikin Yi Da Kashi 8.8% A Lokacin Shugabancin Marigayi Shugaba Ra’isi

An bayyana cewa kashi 8.8 % na rashin aikin yi ya rasgu a kasar Iran a lokacin shugabancin marigayi shahih Ibrahim Ra’isi. Kuma kasar ta

An bayyana cewa kashi 8.8 % na rashin aikin yi ya rasgu a kasar Iran a lokacin shugabancin marigayi shahih Ibrahim Ra’isi. Kuma kasar ta wadatu daga shigo da alkama daga waje. A halin yanzu dukkan alkamar da ake amfani da shi a kasar a cikin gida aka samar da shi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ta nakalto  Amir Riza Wa’iz Ashtiyani yana fadar haka a lokacinda yake hira da wakilin kamfanin dillancin labaran IRNA dangane da irin ci gaban da aka samu a zamanin gwamnati ta 13, ko kuma gwamnatin shugaba marigayi shahid Ra’isi.

Astiyani ya kara da cewa matsalar tsadar kayaki bai takaita ga kasar Iran ba, al-amarin ya kusan game duniya gaba daya. Kuma hatta kasashen da ake ganin suna da tattalin arziki mai karfi a zahiri, suna fama da matsalar tsadar kayaki sai dai bai kai na wasu kasashe muni ba.

Daga karshe Astiyani ya kammala da cewa hukumar FAO ta abinci ta MDD ta bada sanarwa a ranar 8 ga watan Afrilun shekara 2022 kan cewa kimar kayakin abinci ya karu a duniya da kashi 34% idan an kwatanta da shekara ta 2021.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments