Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”.
Taron na gwamnonin gundumomin da suke a gabar ruwan “Caspian” an yi shi ne dai a garin Rasht a gundumar Gilan dake nan Iran.
Mataimakin Fira ministan jamhuriyar Kalmykia ta tarayyar Rasha, ya bayyana jin dadinsa na halartar wannan taron a nan Iran.
A Yau Talata ne dai aka bude wannan taron wanda aka bai wa taken: ” Tekun Caspian A Matsayin Wata Gada Ta Bunkasa Alaka A Cikin Yanki.” Kuma zai ci gaba har zuwa kwanaki biyu masu zuwa.
A wani gefen mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa, ana sa ran halartar shugaban kasar Rasha Vladmir Putin zuwa taron kungiyar kasashen dake gabar ruwan “Caspian” da za a yi a nan Iran a nan gaba.
Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya fada wa kamfanin dillancin labarun “RIA Novosti” cewa; Ziyarar shugaba Valadmir Putin zuwa Iran domin halartar taron kungiyar kasashen gabar tekun “Caspian” yana cikin jadawalin aiki.
Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen na Iran bai bayyana wa’adin gudanar da wannan taron ba.