Search
Close this search box.

Iran: Amurka Ce Babbar Kasa Mai Taimakawa Da Kuma Kare Ayukan Ta’addanci A Yankin Asiya

Jakadan kasar Iran kuma wakilinta a MDD, ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD wasika, inda a cikinta ya maida martani kan zargin da Amurka takewa

Jakadan kasar Iran kuma wakilinta a MDD, ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD wasika, inda a cikinta ya maida martani kan zargin da Amurka takewa kasarsa, ya kuma kara da cewa Amurka ce ‘kawwa uwar gami’ a taiamakawa da kuma samar da ayyukan ta’addanci a yankin Asiya ta kudu da kuma a fagen kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labaran ‘Parstoday’, ya nakalto Amir Sa’id Iravani yana fada a cikin wasikar da ya rubutawa shugaban kwamitin tsaro na MDD a taron sa na ranar 8 ga watan Augusta na shekara ta 2024, yana ce: Tuhumar da Amurka takewa JMI na goyon bayan ayyukan ta’addanci ba gaskiya bane. Sannan ya kara da cewa: Abin kunya ne da kuma ban mamaki ga kasar Amurka, wacce duk duniya ta san cewa ita ce a gaba wajen tallafawa HKI da makamai da kuma goyon baya a kissan kare dangin da take yi a Gaza.

Iravani ya kara da cewa, Amurka tana bawa HKI makamai wadanda take kashe yara da mata a ko wace rana tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata a yankin Gaza. Kuma tana haka ne don ta tabbatar da cewa an tsawaita yakin na Gaza har zuwa lokacinda HKI zata sami nasara a yakin.

Wasikar ta kara da cewa kissan kiyashi na karshen da HKI ta aikata tare da amfani da makaman Amurka shi ne na makarantar Tabi’in a wata unguwa a garin gaza, inda Falasdinawa akalla 100 suka rasa raykansu.

A wani bangaren na wasikar Jakadan ya yi ishara da yadda sojojin Amurka suke mamaye da kasar Siriya da sunan yaki da kungiyar ISIS tun shekara ta 2014, alhali duk duniya ta san cewa gwamnatin kasar Siriya da kawayenta sun kawo karshen Daesh ko ISIS a kasar Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments