Alkalin alkalan kasar Iran Hujjatul Islam Gholamhossein Mohseni Ejei ya yi kare ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa su daina fuska biyu a yin allawadai ko daukar wata kasa yar ta’adda ko mai take hakkin bil’adama da fuska biyu.
Ejei ya bukaci kasashen duniya su yaki taken hakkin bil’adama ba tare da nuna bambanci ba ko fuska biyun ba, kamar yadda wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama wadanda suke samun goyon bayan kasashen yamma suke yi. Yace wasu kasashen yamma suna amfani da kare hakkin bil’adama a matsayin makami kan kasashen bas a dasawa da su.
Alkalin alkalan ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da jakadun kasashen waje a nan birnin Tehran a jiya Laraba, sannan ya kammala da cewa ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa a gaza bai boyu ga kuma ba amma abin mamaki shi ne babu wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa wadanda suke iya yin wani abu na a zo a gani, don dakatar da kissan kiyashin da ke faruwa a gaza, ko kuma a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye.
Yace muna ganin yadda HKI take kashe yara kanana a gaza, tare da amfani da boma bomai masu karfi, amma ba zaka ji duriyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama ko yara suna yin abinda ya dace su yi ba. Amma a baya munga yadda suke tada jijiyoyin wuya idan hakan ya faru a kasashen da kasashen yamma basa dasawa das u.