Avi Lipkin wani marubuci kuma dan siyasa HKI ya bayyana cewa in ba don kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasashen Falasdinu da kuma Lebanon ba, HKI za ta kara mamayar wasu kasashen Larabawa kan wadanda take mamaye da su.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Lipkin ya na fadar haka a hirar da ta hada shi da wata tashar talabijin ta HKI.
Ya kuma kara da cewa, kasashen Lebanon, Masar, Siriya, Jordan, da Saudiya duk suna cikin kasar Isra’ila babba a wajensu.
Wannan kadan kenan daga mummunar ikidun yahudawan Sahyoniyya, dangane da kasashen larabawa. Inda suke riya cewa, wadannan yankunan an yi masu alkawalin mallakarsu kamar yadda yake cikin littafinsu mai tsarki.