ICC ta soki Hungary kan yin watsi da sammacin kame Netanyahu

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin wani taron manema labarai cewa, bai kamata mambobin kotun ICC su yi watsi da hukuncin kotun ba.

Kakakin ya ci gaba da cewa dole ne mambobin kotun su aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke.

Ana sa ran Netanyahu zai isa Budapest a yammacin yau Laraba don ziyarar kwanaki hudu, bisa gayyatar Firaministan Hungary Viktor Orbán.

Shugaban na Hangari mai tsatsauran ra’ayi ya gayyaci takwaransa na Isra’ila duk da tuhumar da ake yi wa Netanyahu a hukumance da laifin amfani da yunwa a matsayin hanyar yaki da kuma aikata laifukan cin zarafin bil’adama a Gaza.

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta bayar da sammacin kama Netanyahu da tsohon ministansa na yaki, Yoav Gallant, bisa zargin laifukan yaki da cin zarafin bil adama a ranar 21 ga Nuwamba, 2024.

An bayar da sammacin ne bayan tantance akwai “kwararen dalilai ” dake cewa Netanyahu da Gallant “da gangan sun hana farar hula a Gaza abuban more rayuwa, ciki har da abinci, ruwa, da magunguna da kuma man fetur da wutar lantarki.” A Gaza.

A matsayinta na mamba a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, dole ne Hungary ta kama Netanyahu da zarar ya isa a tsakiyar nahiyar Turai tare da mika shi ga kotu, saidai duk da haka Hungary, ta fito karara cewa ba za ta mutunta hukunci da bukatun kotun ta ICC ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments