Husi: Guguwar Aqsa Ta Sake Dawo Da Al’adar Jihadi A Tsakanin Al’umma

Shugaban  kungiyar  Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi wanda ya gabatar da jawabi a yau, ya bayyana cewa;Farmakin Guguwar Aqsa, ya sarfado da tunanin

Shugaban  kungiyar  Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi wanda ya gabatar da jawabi a yau, ya bayyana cewa;Farmakin Guguwar Aqsa, ya sarfado da tunanin jihadi a tsakanin al’umma.

Bugu da kari Sayyid Abdulmalik al-husi ya ce; guguwar Aqsa ya kawo karshen akidar yakin HKI ta fara yaki da gama shi a cikin kwanakin kadan, maimakon hakan an tilasta musu yin yaki na tsawon lokaci.

Har ila yau Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce; Ba  Falasdinu ne kadai  HKI take da kwadayin shimfida iko a cikinta ba, tana son shimfida iko a dukkanin kasashen larabawa da ma wannan yankin.

Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce; Abinda HKI take yi a kasa shi ne babban dalili akan cewa tana son yin iko ne da dukkanin wannan yankin.

Haka nan kuma shugaban na kungiyar  Ansarullah ta Yemen ya ce; HKI tana son ganin ita ce kasar da ta fi karfin soja a gabas ta tsakiya da zai ba ta damar mamaye wannan yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments