Hukumomin Lafiya Na Duniya Na Gargadi Kan Matsalilin Kiwon Lafiya A Gaza

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, akwai babban hadarin kamuwa da cutar shan inna a Gaza da ma gaba da iyakokinta, saboda yanayin rashin lafiya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, akwai babban hadarin kamuwa da cutar shan inna a Gaza da ma gaba da iyakokinta, saboda yanayin rashin lafiya da tsaftar muhalli a yankin Falasdinawa da ke fama da yaƙi.

Ayadil Saparbekov, jagoran tawagar gaggawa na kiwon lafiya a WHO a Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ya ce an ware nau’in cutar shan inna ta 2 da aka samu daga samfuran muhalli daga najasa a Gaza.

“Akwai babban hadari kan yaduwar cutar shan inna a Zirin Gaza, ba wai kawai don gano cutar ba amma saboda tsananin yanayin da ake ciki na tsaftar ruwa,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai a Geneva ta hanyar bidiyo daga Kudus.

“Hakanan cutar tana iya yaɗuwa a duniya, a wani matsayi mai girma.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments