Hukumar UNRWA ta sanar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya da ke kan hanyar zuwa Gaza
Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ga ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta bayyana cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi luguden wuta kan ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya da ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Gaza a jiya Lahadi.
Babban daraktan Hukumar Ba Da Agaji da Ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ga ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” Philippe Lazzarini ya bayyana a cikin wani rubutu a dandalin “X” cewa: Ayarin motocin hukumarsu sun fuskanci harbe-harbe da harsasai a lokacin da suke jiran shiga cikin shingen binciken sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a tsakiyar Zirin Gaza.
Ya kara da cewa: Wannan ya faru ne a daidai lokacin da tawagar Hukumar ke tafiya a cikin mota mai sulke mai dauke da alamomin Majalisar Dinkin Duniya da kuma sanye da rigunan Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ci gaba da cewa: Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun bude wuta mai tsanani kan ayarin motocin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Gaza a ranar Lahadi.