Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta “UNRWA” ta ce: Kashi 9 cikin 10 na Falasdinawa a Gaza an tilasta musu gudun hijira
Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Kashi 9 daga cikin 10 na Falasdinawa an tilasta musu gudun hijira daga yankin Zirin Gaza, wanda ke fama da mummunan yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan yankin yau tsawon rana ta 295 a jere.
Hukumar ta UNRWA ta jaddada a cikin wani sakon da ta wallafa a dandalin X cewa: Kashi 9 cikin mutane 10 na Gaza – mai yawan jama’a kusan miliyan 2.3 – an tilasta musu yin gudun hijira.
Ta kara da cewa: Iyalan da suka rasa matsugunansu na neman matsuguni a duk inda suke, walau a makarantu masu cunkoson jama’a, ko a wuraren rugujajjun gine-gine ko kafa tantuna a kan yashi ko kuma a kan tarin shara wato bola, hukumar tana mai jaddada cewa, babu daya daga cikin wadannan wuraren da ke da aminci kuma mutane ba su da wurin zuwa.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 ce, rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza, wanda a halin yanzu ya yi sanadin shahadar dubun dubatar Falasdinawa da raunata wasu dubbai gami da bacewar dubbai na daban kuma yawancinsu yara da mata.