Hukumar ‘UNESCO’ Ta Nuna Damuwarta Ga Yanayin Rayuwar Yara A Garin Rafa Bayan Mamayar Sojojin HKI

Hukuma mai kula da yara ta MDD wato UNECO ta bayyana damuwarta da yadda yara kanana a garin Rafah na kudancin zirin gaza suke rayuwa

Hukuma mai kula da yara ta MDD wato UNECO ta bayyana damuwarta da yadda yara kanana a garin Rafah na kudancin zirin gaza suke rayuwa bayan mamayar da sojojin HKI suka yiwa kofar Rafa da kuma ta karim Abu saleh wadanda ta nan ne kawai ake shigar da abinci da magunguna da kuma kayakin bukatu na yau da kullum a gaza.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto hukumar tana fadar haka a jiya Lahadi, ta kuma kara da cewa akalla yara kimani 600 ne suke rayuwa a garin Rafa inda a halin yanzu sojojin HKI suke fafatawa da mayakan kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa.

Banda haka hukumar da kara da cewa babu wani wuri mai amince da ya rage a gaza, inda yara da iyayensu zasu sami aminci a rayuwarsu, wannan tare da karanci ko kuma rashin abinci mai gina jiki da suke fama da su.

A ranar litinin 6 ga watan Mayun da muke ciki ne sojojin HKI suka kwace iko da kofar Rafah na zirin gaza tare da bawa Falasdinawa da suke rayuwa a garin umurni na su fice daga garin su koma tsakiyar Gaza. Sannan a ranar tarlatan da ta gabace ce sojojin suka fara kai farmaki ta sama da ta kasa a kan falasdinawa a garin, wannan duk tare da korafe korafen da kasashen duniya suka yi, na mummunar illar da farwa garin Rafah zai jawo ga al-ummar Falasdinu kimani miliyon 1.3 da suke rayuwa a garin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments