Hukumar Sararin Samania Na Kasar Iran Tana Da Taurarin Dan’adam 14 Wadanda zata Cillasu Sama Nan Gaba

Shugabann hukumar sararin samaniya na kasar Iran Hasan Salariyeh ya bada sanarwan cewa hukumarsa tana da taurarin dan’adam har guda 14 wadanda suke jiran a

Shugabann hukumar sararin samaniya na kasar Iran Hasan Salariyeh ya bada sanarwan cewa hukumarsa tana da taurarin dan’adam har guda 14 wadanda suke jiran a cillasu zuwa sararin samaniya nan gaba. Sannan akwai wasu 30 ana cikin aikin kerasu. 20 daga cikinsu kamfanoni masu zaman kansu ne suke keresu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a farkon wannan shekarar hukumar ta cilla tauraron dan’adam wanda ake kira Mahda tare da amfani da roka mai suna ‘Simorgh’ tare da nasara, zuwa kilomita 450-500 a sararin samanin.

Kasar Iran dai na daga daga cikin kasashe 10 a duniya wadanda suke da fasahar kerawa da kuma cilla taurarin yan’adam daga cikin gida ba tare da neman atimako daga waje ba.

Labarin ya kara da cewa a cikin shekaru 3 na gwamnatin marigayi Shahid  Ibrahim Ra’isi, hukumar ta cilla taurarin dan’adam har guda 12 wanda shi ne adadin taurarin da aka cilla a gwamnatocin da suka shude.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments