Hukumar Mahajjata Ta Najeriya {NAHCON} Ta Bayyana Farashin Aikin Hajji Na Shekara Ta 2025

Hukumar mahajjata ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da farshin aikin Hajjin bana na naira miliyon 8.7 ga mahajja daga kudancin kasar sannan a bangaren mahajjata

Hukumar mahajjata ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da farshin aikin Hajjin bana na naira miliyon 8.7 ga mahajja daga kudancin kasar sannan a bangaren mahajjata daga jihohin Borno da Adamawa kuma zasu biya miliyon 8.3.

Jiridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Shugaban hukumar mahajjatan na kasar Alhaji Abdullahi Usman ya na fadar haka ta bakin mataimakin daraktan ya da labarai na hukumar Fatimah Usara a yau Litinin a Abuja.

Alhaji Usman ya kammala da cewa sauran jihohin arewacin kasar za su biya naira miliyon 8.4 saboda aikin hajjin Bana kan ko wani mahajjaci..

Daga karshen shugaban hukumar ya godewa duk wadanda suka taimaka don fitar da farashin aikin hajjin na bana, wadanda suka hada da ofishin shugaban kasa da kuma ma’aikatar hukumarsa.

Labarin ya kara da cewa, wanda yake son karin bayani kan yadda aka lissafa kudaden ayyukan Hajji na Bana, yana iya komawa zuwa ga shafin yanar gizo na hukumar.

Sai dai hukumar bata bayyana yauce ne za’a fara tattara kudaden aikin hajji ba da kuma ranar da za’a rufe biyan kudaden.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments