A rahoton da Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta fitar a ranar Talatar da ta gabata ta bayyana cewa sama da ‘yan Sudan miliyan 10 ne suka rasa matsugunansu daga garuruwa da kauyuka tun farkon bullar yaki a kasar a tsakiyar watan Afrilun shekara ta 2023, yayin da yunwa ke yaduwa a tsakanin al’ummar kasar.
Rahoton ya kara da cewa: Adadin mutanen da suka rasa matsugunansu ya kai kashi 20 cikin dari na al’ummar Sudan. Sannan Hukumar a cikin wani rahoto da take fitarwa wata-wata ta ce: Sama da mutane miliyan 2.2 ne suka tsere zuwa wasu kasashe musamman wadanda suke makwabtaka da su tun bayan barkewar yakin kasar, yayin da kimanin miliyan 7.8 suka rasa matsugunansu. Akwai kuma wasu miliyan 2.8 da suka rasa matsugunansu saboda tashe-tashen hankula a kasar.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bayar da rahoton cewa, rabin al’ummar kasar Sudan kimanin miliyan 50 na fuskantar matsalar yunwa da kuma bukatar agajin jin kai fiye da kowace kasa a duniya.