Search
Close this search box.

Hukumar Kula Da Fursinoni Falasdinawa Ta Bada Sanarwan Kama Mutane Akalla 9000 Tun Bayan Fara Yaki A Gaza

Hukuma mai kula da furinonin Falasdinawa ta bada sanarwan cewa tunn bayan fara yakin tufanul Aksa a gaza, sojojin HKI sun kama Falasdinawa 9280 a

Hukuma mai kula da furinonin Falasdinawa ta bada sanarwan cewa tunn bayan fara yakin tufanul Aksa a gaza, sojojin HKI sun kama Falasdinawa 9280 a yankin yamma da kogin Jordan kadai.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto hukumar Fursinoni Falasdinawa na fadar haka a safiyar yau Laraba. Kuma ta  kara da cewa

Hukumar ta kara da cewa a ranar Litinin da ta gabata kadai sojojin yahudawan sun kama falasdinawa 90 a yankin yamma da kogin Jordan, daga cikinsu har da mata da yara sun tafi da su.

Tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekaran da ta gabata ne, wasu daga cikin falasdinawa a yankin suna fara tada kayan baya, suna kuma fafatawa da sojojin yahudawa a yankin, kuma yankunan da suka fi tada kayan bayan dai sun hada da garuruwan Nablos, Toolkaram, Jinin da kuma Khalil.

A yau Laraba ma, rahoton ya bayyana cewa ya zuwa lokacin bada wannan rahoton sojojin yahudawan sun kama Falasdinawa 35.

A zirin gaka kuma inda ya zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa kimani 38, a yau Laraba ma sun ci gaba da barin wuta ta sama da kasa da kuma ruwa kan wurare daban daban a yankin.

Hukumomin MDD da dama sun bayyana cewa har yanzun basu sami nasar isar da kayakin agajin da suke tare da su don mutanen Gaza ba. Saboda sojojin yahudawan sun toshe dukkan hanyoyin shigar da kayakin agaji cikin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments