Search
Close this search box.

Hukumar Falasdinawa Ta Aike Da Sakonni Wasiku Tana Neman Taka Burki Ga ‘Yan Sahayoniyya

Hukumar cin kwarya-kwaryar Falasdinawa ta aike da wasiku har 3 ga jami’an Majalisar Dinkin Duniya tana kiransu da su dauki mataki kan kashe-kashen gillar da

Hukumar cin kwarya-kwaryar Falasdinawa ta aike da wasiku har 3 ga jami’an Majalisar Dinkin Duniya tana kiransu da su dauki mataki kan kashe-kashen gillar da yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da yi kan Falasdinawa

Wakilin dindindin na Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya aike da wasiku har sau uku zuwa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, da Shugaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, Dennis Francis, da Shugaban Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya jakadan kasar Saliyo a wannan watan, dangane da kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take yi wa al’ummar Falastinu da ba su da kariya musamman na baya-bayan nan a makarantar Al-Ta’bi’een da ke unguwar Al-Daraj da ke dauke da ‘yan gudun hijira da ya lashe rayukan mutane fiye da 100 tare da jikkatan wasu daruruwa na daban.

Mansour ya ce; Duniya ba za ta ci gaba da nuna halin ko-in-kula ga irin wannan ta’asa da cin mutuncin bil’adama ba, kuma kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ba zai yiwu ya nade hannu yana ganin irin wannan ayyukan dabbanci na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba, amma a daidai lokacin da ake batun mutunta dokokin kasa da kasa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da yin fatali da yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya da kudurorinta gami da rashin mutunta wani abu daga cikin ka’idojin dokokin kasa da kasa. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments