Hukumar DSS Ta Najeriya Ta Saki Sowore Bayan Kama Shi

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya ce an tsare shi na ɗan lokaci a filin jirgin saman Murtala

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya ce an tsare shi na ɗan lokaci a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas bayan dawowarsa daga Amurka.

Sowore, ya bayyana hakan a shafinsa na X a safiyar ranar Lahadi, inda ya ce an sake shi bayan shafe mintuna kaɗan a hannu jami’an tsaro.

Sowore, wanda ya jagoranci zanga-zangar #RevolutionNow, ya ce jami’an shige da fice na Najeriya, sun ƙwace masa fasfo tare da shaida masa cewa an ba su umarnin tsare shi.

“Na iso Najeriya daga Amurka a filin jirgin sama na Legas; da na isa wajen jami’an shige da fice, sun ƙwace min fasfo suka ce an ba su umarnin tsare ni.

Sai dai har zuwa yanzu ba a tabbatar da wanda ya bayar da umarnin tsare shi ba.

Amma rahotanni sun nuna cewar jami’an hukumar tsaro ta DSS ne suka kama shi, sai dai DSS musanta kama Sowore da ake zargin jami’anta da yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments