Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasar Iran ko (Iran Red Crescent) IRCS Mir Hussain Koliyand, a cikin watan wasikan da ya rubutawa shugaban ‘ American Red Cross’ Clift Holt, da farko ya taya mutanen kasar musamman wadanda musibar gobarar daji ta sahaf a jihar Calfonia, ilhin abinda ya samesu, sannan ya ce yana bukata hukukarsa a shirye take ta taimaka, don kawo karshen gobarar dajin da ta fadawa jihar musamman a birnin Los-‘Angeles na kudancin jihar ta Calfonia.
A jiya jumma’a kadai an bawa mutane kimani 100,000 umurnin ficewa daga yankunan da su a jihar, saboda wutan daji da ta cinye mafi yan birnin L.A.
Rahotonni sun bayyana cewa akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, sanadiyyar gobarar, ya zuwa yanzu.
Amma kwararru suna ganin cewa ba za’a gane adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar gabatar ba, sai an kawo karshen gobarar.
Wutan daji sun tashi a warare akalla 6 a jihar Calfiniya, a ranar Jumma’a kuma hukumar kwana-kwana ta Jihar kasa kashe gobarar, sanadiyyar isaka mai karfi take taimakawa yaduwar wutar.