Hukumar Ba Da Agaji Ta Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kakkausar Suka Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Gaza

Hukumar bayar da agajin jin kai ta Majalisar Dinkin Dunya {OCHA} ta bayyana shirin da aka sanar na mamaye Gaza da cewa; Zai haifar da

Hukumar bayar da agajin jin kai ta Majalisar Dinkin Dunya {OCHA} ta bayyana shirin da aka sanar na mamaye Gaza da cewa; Zai haifar da mummunan sakamako na jin kai

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya yi gargadin cewa: Shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sanar na mamaye daukacin birnin Gaza zai yi mummunan tasiri ga Falasdinawa da aka hana su samun kayan agajin jin kai.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto ofishin OCHA da ke yankin Falasdinawa da aka mamaye tana fadar haka a cikin wata sanarwa a jiya Litinin cewa: Kimanin kashi 86% na yankin na zirin Gaza na karkashin umarnin gudun hijira ko kuma fada a cikin yankunan da sojojin mamayar Isra’ila ke iko da su.

Ta bayyana cewa: “Sauran wuraren da suka hada da wasu sassan birnin Gaza da kuma wasu sassan gabar tekun kudancin kasar – sun cika cunkoso da rashin kayan aiki don samar da rayuwa mai inganci.”

Ta jaddada cewa: “Shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na karfafa ayyukan soji a birnin Gaza zai yi mummunan tasiri ga al’ummar da tuni ke fama da gajiya, rashin abinci mai gina jiki, hasara, da rashin matsugunai da kuma hana kayayyakin agaji na rayuwa.”

Ofishin na OCHA ya bayyana cewa: “Tilastawa dubban daruruwan mutane gudun hijira (daga arewacin zirin Gaza) zuwa kudanci wani shiri ne na ƙarin bala’i kuma yana iya zama gudun hijira na tilasta.” An lura cewa; Asibitoci a kudancin zirin Gaza “suna aiki da iyakan karfinsu, kuma karbar ƙarin marasa lafiya daga arewa zai haifar da mummunan sakamako.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted