Kasar Honduras ta yi barazanar korar sansanonin sojin Amurka daga kasarta idan har aka kai ga korar bakin haure na fitar rai da Trump ya yi barazana
Shugabar kasar Honduras Xiomara Castro ta yi gargadin cewa za ta kawo karshen zaman sansanonin sojin Amurka a kasarta, idan zababben shugaban kasar Donald Trump ya aiwatar da barazanarsa na korar bakin haure ‘yan kasar Honduras a lokacin da ya hau kan karagar mulkin Amurka a ranar 20 ga wannan wata na Janairu.
A cikin jawabin da ta gabatar a jiya Laraba, Castro ta ce: Ayyukan nuna gaba da kiyayya kamar korar jama’a za su sa ya zama dole a sake yin nazari kan yarjejeniyar hadin gwiwa da Amurka, musamman a fannin soji, kamar yadda Amurka ke kula da sansanonin kasar ba tare da biyan kudaden haraji ba.
Kasar Amurka dai tana da sansanin soji a jihar Comayagua na kasar Honduras tun a shekara ta 1980, wanda aka kafa don yakar ƙungiyoyin gurguzu. Castro ta kara da cewa wadannan sansanonin za su rasa izinin ci gaba da wanzuwarsu a Honduras idan Amurka ta aiwatar da manufar korar bakin hauren.