Shugaban kungiyar Agajin ta Falasdinawa Unrwa ya bayyana yadda HKI take kokarin ganin an rusa kungiyar tasu da kawo karshen ayyukan da take yi musamman a Gaza.
Ita dai Unrwa tana a matsayin mafi girman kungiyoyin agajin Falasdinawa a Gaza wacce take da ma’aikata 13,000, da a cikin yanayin yaki take ragewa Falasdinawa radadi.
Sai dai daga lokacin da HKI ta shelanta yaki akan al’ummar Gaza, adadin ma’aikatan kungiyar ya ragu zuwa 3000 kadai.
Baya ga raba kayan abinci, kungiyar tana kuma da ajujuwa da makarantu da take koyar da Falasdinawa, haka nan kuma ayyukan kiwon lafiya.
Shugaban kungiyar Phillip Lazarani ya soki HKI saboda yadda take kawo cikas wajen aikewa da kayan agaji zuwa yankin na Gaza.
A karshen watan Janairu ne wasu kasashen turai da su ka hada Birtaniya, Jamus da Amurka su ka sanar da dakatar da bai wa wannan kungiyar ta MDD taimako, saboda biyewa riwayar HKI na cewa wasu daga cikin ma’aikatan Unrwa sun taka rawa a harin raanr 7 ga watan Oktoba.