HKI Tana Cikin Tsaka Mai Wuya Duk Tare Da Goyon Bayan Da Take Samu Daga Kasashen Yamma

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa a halin yanzu HKI bata da karfin kare mutanen kasarta, saboda makaman makiya suna

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa a halin yanzu HKI bata da karfin kare mutanen kasarta, saboda makaman makiya suna isa har tsakiyar kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kan’ani yana fadar haka a safiyar yau Litinin, ya kuma kara da cewa hare-haren da dakarun Hizbullah suka kai kan HKI wanda aka sanya masa suna “hare haren 40’ sun tabbatar da cewa hatta yahudawan da suke rayuwa a babban birnin kasar ba sa cikin amince daga makaman Hizbulla da kuma sauran kasashe masu gwagwarmaya a yankin.

A safiyar jiya Lahadi ce dakarun kungiyar Hizbulla suka cilla makamai masu linzami kimani 320 kan wurare daban daban a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye, daga cikin har da wasu wurare a birnin Tel’aviv babban birnin haramtacciyar kasar.

Shugaban kungiyar Sayid Hassan Nasarallah ya tabbatar da cewa ‘hareharen 40’ sun sami nasara, don makaman kungiyar sun sami bararsu kamar yadda aka tsara.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments