HKI Ta Tilastawa Iyalai 10 Ficewa Daga Gidajensu A Sansanin ‘Yan Hijira Na Nabilus

 Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu.

 Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu.

Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus.

A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa; Sojojin HKI suna da shirin kai hare-hare ta kasa a cikin yankin Gaza.

Jaridar “Wall Street Journal” ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya za su ci gaba da zama a yankunan da su ka shiga a cikin Gaza, sannan kuma su kai wasu sabbin hare-hare ta kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments