Ma’aikatar Ilmi a Gaza ta bada rahoton cewa a cikin watanni 10 da suka gabata, wato tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, sojojin HKI sun kashe daliban jami’i’o’i a Gaza da kuma yamma da kogin Jordan wadanda yawansu ya fi dubu 10.
Tasahr talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto rahoton yana cewa sojojin yahudawan sun jikata wasu daliban jami’o’i har kimani 16 a cikin wannan lokacin. Sannan malamansu da kuma jami’an harkokin gudanarwa fiye da 500 suka kashe, banada haka wasu 3000 ne suka ji rauni.
Rahoton ya kara da cewa an rusa makarantu 62 a Gaza a yayinda wasu 119 kuma an lalatasu. Rahoton ya kara da cewa malaman kimiya da kuma wadanda suka kai matsayin Ferfesa 107 suka yi shahada.
Rahoton ya ce, hatta makarantu wadanda suke karakshin ‘hukumar bada agaji ga Falasdinawa ta MDD (UNRWA) a Gaza basu tsira ba.
Rahoton ya kammala da cewa a wannan shekarar dai an hana daliban 6000 zuwa manya manyan makarantu saboda yaki.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar ta 2023 ya zuwa yanzu falasdinawa kimani 40,000 ne suka yi shahada a yayida wasu kimani 91,000 suka jikata, sanna akwai wasu da yawa a karkashin kasa wadanda ba a san inda suke ba.