A jiya Asabar ce jiragen yakin HKI suka yi luguden wuta kan Falasdinawa a Gaza wadanda suke bikin aure duk tare da mummunan halin da suke rayuwa a yankin, inda ta maida bikin auren bakin ciki.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Falasdinawan wadanda suke samun mafaka a wata makaranta a cikin birnin Gaza, suna gudanar da bikin aure in da da dama daga cikin wadanda suka halarci bikin suka yi shahada ko suka ji rauni.
Wannan yana daga cikin munanan hare-haren da sojojin yahudawan suka kai kan Falasdinawa bayan abinda Trump ya kira tsagaita budewa juna wuta a tsakanin Hamas da kuma gwamnatin HKI.
Rahotannin sun bayyana cewa tun bayan yerjeniyar tsagaita wutan da bangarorin biyu suka cimma a ranar 10 ga watan Octoban na wannan shekara mai karewa sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawafiye da 1300 sannan tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 kuma, adadin wadanda suka yi shahada sun wuce dubu 70,000.