Sojojin HKI sun tabbatar da cewa garkuwan makamai masu linzami na kasar wanda ake kira (iron Dome) sun gaza aiki kamar yadda ya dace a yakin kwanaki 12 da suka kaiwa kasar Iran a cikin watan Yulin da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto daga wata majiya, ta sojojin HKI kan cewa a halin yanzu sun kawo wano garkuwan wanda aka yi masa wasu karin ayyuka, wanda har yanzun ba’a tabbatar da cewa zai yi aiki kamar yadda ake so ba.
Labarin ya tabbatar da cewa babu tabbas idan wanda aka kawo a halin yanzo zai yi aikin na kare kasar daga makaman masu linzami samfurin bilistic na kasar Iran a yaki na gaba ba.