Hizbullah Ta Yi Ruwan Rokoki Kan Rundunar Sojojin HKI A Arewacin Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa ta yi barin wuta kan wata rundunar sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa ta yi barin wuta kan wata rundunar sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye a ranar Asabar inda ta yi masu barna mai yawa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani bayanin da kungiyar ta fitar yana cewa sun yi amafani makaman ‘Drones’ ko jiragen yaki masu kunan bakin wake, a kan barikin Shraga dake arewacin garin Akka, wanda ya kasance cibiyar rundunar Golani ta HKI wacce ta shahara a mummunan ayyukanta a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Labarin ya kara da cewa makaman sun sami bararsu kamar yadda aka tsare. Har’ila yau sun yi amfani da wani makami mai linzami mai suna Kamikaze inda shima ya sami bararsa a kan rundunar ta Golani har sau biyu.

Rundunar Golani dai ta aikata, kuma tana ci gaba da aikata kissan kiyashi masu yawa a kasar Falasdinu da aka mamaye tun shekara ta 1948, a lokacinda yahudawan sahyoniyya suka mamaye kasar Falasdinu.

Haka ma dakarun hizbullah sun kara da wannan rundunar a shekara ta 2000 da kuma shekara ta 2006 a kudancin kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments