Hizbullah ta kirayi gwamnatin Lebanon da ta dauki mataki kan hare-haren Isra’ila

Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona

Wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ba da fifiko wajen dakatar da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon.

A cewar Al-Mayadeen Hassan Fadlallah mamba a bangaren Hizbullah a majalisar dokokin kasar Labanon ya ce: Dakatar da wuce gona da iri kan kasar Labanon wani muhimmin al’amari ne na kasa da ya zama wajibi a sanya shi cikin ajandar gwamnatin Lebanon.

Ya kara da cewa: Al’ummar kasar Labanon suna fuskantar wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan tare da yin kira ga gwamnati da ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dakile wannan ta’addanci.

Fadlallah dai ya dauki babbar matsalar kasar Labanon a matsayin mamaya da kuma keta hurumin kasar, yana mai jaddada cewa wasu na son jefa kasar cikin rudani da ruguza karfin da kasar ta Lebanon ke da shi na tunkarar mulkin kama-karya na kasashen waje. Irin wadannan ayyuka sun saba wa muradun kasar Lebanon, kuma sun yi daidai da muradin makiya.

Hassan Fadlallah ya musanta ikirarin da wasu kafafen yada labarai suka yi cewa Hizbullah na amfani da tashar jiragen ruwa na Beirut wajen safarar makamai, ya kuma yi kira ga mahukuntan kasar Lebanon da su dauki mataki kan masu yada wadannan karairayi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments