Hizbullah Ta Kai Wa Ma’aikatar Yakin HKI Hari A Karon Farko

A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Laraba ta sanar da cewa, ta kai hari da jirgin sama maras matuki akan ma’aikatar

A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Laraba ta sanar da cewa, ta kai hari da jirgin sama maras matuki akan ma’aikatar yakin HKI, inda nan ne manyan hafsoshin sojojin Sahayonina suke. Haka nan kuma daga nan ne ake tafiyar da yake-yaken da HKI take yi.

A sanarwar da kungiyar Hizbullah ta fitar a jiya Laraba ta bayyana cewa; Saboda taimakawa mutanen Gaza, masu jajurcewa, da kuma gwagwarmayarsu maijarunta, haka nan kuma domin kare Lebanon da al’ummarta, kuma a karkashin farmakin da muke kai wa mai suna; Khaibar” sannan kuma da taken; “Labbaika Ya Nasrallah”  da misalin karfe:  3;30 bayan azahar gwgawarmayar musulunci ta kai hari da jiragen sama marasa matuki akan ma’aikatar yaki wanda shi ne karo na farko.

Sanarwar ta kuma ce a cikin wannan ma’aikatar ne manyan hafsoshin sojan ‘yan sahayoniya suke, kuma daga can ne ake tafiyar da yake-yake.

Bugu da kari kungiyar Hizbullah ta ce harin ya yi nasara domin jiragen da aka tura sun sauka inda aka tura su.

Wata sanawar ta daban ta Hizbullah ta ce ta kai wani harin na biyu  akan da makami mai linzami samfurin “Ballistic” akan ma’aikatar yakin ta ‘yan sahayoniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments