Mayakan kungiyar Hizbulla ta kasar Lebanon sun kai hare hare kan cibiyar na’urar Rada da kuma sansanonin HKI guda uku a arewacin kasar falasdinu da aka mamaye a jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya litinin mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun cilla makamai masu linzami har 4 kan cibiyar na’urar Rada ta HKI.
Har’ila yau labaran sun kara da cewa, sun kai farmaki kan taron sojojin HKI a cikin sansanin sojojinta da ke ‘Hanitaa’ dake arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, tare da amfani da makamai masu linzami da kuma ikgwa. A wani labarin kuma sun kai irin wadannan hare hare kan sojojin yahudawan a garin Ruwistaat Al-ilim dake kan tuddan Kafarshuda na kasar Lebanon da aka mamaye.