A wani zanga-zangar lumana da suka gabatar a jiya Asabar masu goyon bayan kungiyar Hizbullah sun yi kira ga gwamnatin kasar Lebanon kada ta bari Amurka da HKI su zama su ne ke jajjuya al-amuran kasar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmood Qamati shugaban kwamitin siyasa na kungiyar Hizbullah ya na fadar haka a jiya Asabar, a kan babban titin da ya ke zuwa tashar jiragen sama na birnin Beirut babban birnin kasar kasar, wato Rafiqul Hariri INT. Airport, inda mabiya kungiyar suka yi gaggami, don nuna rashin amincewar da hana jiragen saman Iran sake sauka a tasahar.
Qamati ya kara da cewa bai kamata HKI tayiwa jiragen saman Iran masu zuwa beiru barazana, sannan ita kuma gwamnatin kasar Lebanon ta hana jiragen Iran sauka a Lebanon ba.
Kafin haka dai, HKI ta yi barazanar kakkabo dukkan jiragen fasinja masu zuwa kasar Lebanon don suna kawowa kungiyar Hizbullah makamai ko kudide.
Sannan maimakon gwamnatin kasar Lebanon ta san yadda zata yi ta tabbatar HKI al-amarin ba haka ba. Ta kare kasar Iran sai ta dakatar da dukkan jiragen fasinja masu zuwa Beirut daga Iran don wai kada HKI ta kakkabosu.