Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon

Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda

Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda al’ummar yankin ke fuskantar barazanar wanzuwa da kuma ‘yancinsu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na yau da kullun, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da na larabawa, a wani bangare na yunkurin sake fasalin yankin da kasar Lebanon.

Babban abin da kungiyar tafi nuna takaicinta  akansa shi ne amincewar da gwamnatin Lebanon ta yi a baya-bayan nan da  shawarar da manzon Amurka Tom Barrack ya gabatar.

Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani sabon salo na saba alkawuran ministocin gwamnati da kuma karya rantsuwar da shugaban kasa ya yi. Ta nanata cewa takardar ta sabawa ka’idojin yarjejeniyar Taif, wadda ta tabbatar da ‘yancin kare kai da kuma kiyaye ‘yancin kasar Lebanon.

Kungiyar ta bayyana amincewar da gwamnatin kasar ta yi wa takardar  Amurka a matsayin rashin gaskiya,” tana mai gargadin cewa irin wannan matsayi a file yake kan cewa ya keta yarjejeniyar kasa” tare da yin barazanar kwace wa kasar Lebanon daya daga cikin manyan hanyoyin karfinta, wato gwagwarmayar sa kai domin kare kasa.

Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa, karfinta na soji wani babban jigo ne kuma ginshiki a fagen tsaron kasar Lbanon, musamman ma ganin yadda ake samun karuwar barazana da kuma rashin wani tabbataccen lamuni na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted