Kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hare-hare da dama da jirage marasa matuka da makamai masu linzami kan wurare da sansanonin soji a yankin Tel-Aviv da kuma kudancin Isra’ila.
A Isra’ila, an yi ta jin karar gargadi a yankuna da dama, musamman a bayan birnin Tel Aviv, in ji sojojin, inda suka ba da rahoton harba makamai masu linzami 160 daga makwabciyar kasar Lebanon, wadanda aka kakkabo wasu daga cikinsu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare kan kasar Labanon.
A cewar kafafen yada labarai na yaren Hebrew, akalla ‘yan Isra’ila 10 ne suka jikkata a Petah Tikva da ke gabashin Tel Aviv, da kuma Haifa da Nahariya bayan da makaman roka suka afkawa wadannan yankuna.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun kuma bayar da rahoton cewa, an ji karar fashewar wasu abubuwa a tsakiyar birnin Tel Aviv, sakamakon saukar rokoki da aka harba daga kasar Lebanon.
Tun a watan Oktoban shekarar 2023 ne Isra’ila ke kai hari kan kasar Labanon, lokacin da ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza.
Akalla mutane 3,600 ne hare-haren Isra’ila suka kashe, yayin da wasu 15,200 suka jikkata tun bayan barkewar rikicin a bara, a cewar ma’aikatar lafiya Lebanon.