Kungiyar Hezbollah ta sanar da kai jerin hare-hare a jiya Alhamis kan wuraren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kafa tungarsu, wanda kuma hakan ya zo domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu a Gaza da kuma kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa.
Ayyukan sun hada da harba makamai masu linzami da kuma jiragen marsa matuka kan wuraren na sojojin, wanda sashen tsaron sama nakungiyar ya yi, wanda shi ne karo na biyu cikin kasa da sa’o’i 24.
Hezbollah ta ce harin ya zo ne a matsayin mayar da martani ga keta sararin samaniyar Lebanon da Isra’ila ta yi, tare da tabbatar da cewa jiragen na Hezbollah sun yi mummunar barna a kan sansanonin sojin yahudawan Isra’ila.
A yammacin ranar Alhamis ne kungiyar Hizbullah ta sanar da shahadar daya daga cikin mayakanta, wanda ya shiga cikin jerin shahidai na gwagwarmayar ‘yantar da Quds daga mamayar yahudawa.
Shahidin na kungiyar Hizbullah shi ne bdallah Mohammed Fakih “Abes,” an haife shi a shekara ta 2000 a garin Rab El Thalathine.
Kungiyar ta kuma wallafa hotunan wani samame da mayakanta suka kaddamar a makon da ya gabata, inda ta yi amfani da wani jirgin sama mara matuki domin kai hari kan wata na’urar sarrafa makaman kariya da jiragen yakin sojin Isra’ila a kusa da kan iyakokin Lebanon.