Hezbollah ta kai hari a kan filayen jiragen saman sojan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon ta Hizbullah  na ci gaba da gudanar da ayyukanta na mara baya ga al’ummar Gaza, da kuma mayar da

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon ta Hizbullah  na ci gaba da gudanar da ayyukanta na mara baya ga al’ummar Gaza, da kuma mayar da martani ga hare-haren  Isra’ila kan Lebanon.

Mayakan kungiyar sun kai hari a filin jirgin saman soja na Megiddo da ke yammacin Afula da kuma sansanin Ramat David na sojojin mamaya na Isra’ila.

A ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu masu tsayin daka a Zirin Gaza, da kuma kare kasar Labanon da ‘yan kasar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da kaddamar da hare-hare da dama kan a arewacin Falasdinu da yahudawa suka mamaye.

Harin na Hezbollah ya nufi filin jirgin saman soja na Megiddo da ke yammacin Afula har sau uku tare da harba rokoki samfurin Fadi-1 da Fadi-2.

An kuma kai wasu Hare-haren a kan sansanin sojin Isra’ila na  Ramat David da filin jirgin saman soja na salvo da makami mai linzami, da kuma  sansanin Amos, da ke a matsayin babbar cibiyar tallafin kayan yaki da sufuri na sojin Isra’ila a yankin arewacin kasar.

Tun da farko wakilin tashar Al Mayadeen a kudancin kasar Labanon ya rawaito cewa an harba wasu manyan rokoki guda hudu zuwa yankunan Falasdinawa da yahudawa suka mamaye.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, hare-haren Hizbullah sun hada yankuna da dama daga ciki har da Golan,  Afula, Gingar, Yafia al-Naseriyya, Migdal HaEmek, Mazraa, da yankunan al-Jalil da Haifa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments