Harin Wuce Gona Da Irin Sojojin ‘Yan Sahayoniyya Ya Lashe Rayukan Falasdinawa 10

Falasdinawa akalla 10 ne suka yi shahada wasu 30 kuma suka samu raunuka a harin da sojojin mamaya suka kai kan wata makaranta a sansanin

Falasdinawa akalla 10 ne suka yi shahada wasu 30 kuma suka samu raunuka a harin da sojojin mamaya suka kai kan wata makaranta a sansanin Jabaliya

Falasdinawa 10 ne suka yi shahada, wasu 30 kuma suka jikkata, a jiya Litinin, sakamakon luguden wuta da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a kan makarantar share fage da ke Jabaliya da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.

Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar da cewa: Tawagar likitocin sun samu nasarar gano shahidai 10 da wasu da dama da suka samu raunuka a wani harin makami mai linzami da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan makarantar share fage ta Jabaliya da ke filin makarantar Al-Fawqa, wadda cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ta UNRWA ce ta mayar da ita mafaka ga ‘yan gudun hijira a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza.

Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Falasdinawa 57 ne suka yi shahada a hare-haren da ‘yan mamaya suka kai a Zirin Gaza tun daga wayewar jiya Litinin, kuma 44 daga cikinsu a arewacin yankin.

Hakazalika, hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence ta tabbatar da cewa sama da Falasdinawa 600 ne suka yi shahada tun bayan fara kai harin wuce gona da iri kan sansanin Jabaliya a ranar 6 ga wannan wata na Oktoba, yayin da shahidai da dama ke karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments