Harin Ta’addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Biyar Tare Da Jikkata Wasu Ashirin Na Daban A Somaliya

Akalla mutane 5 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a Somaliya sakamakon fashewar wani bam da aka dana a wata mota a

Akalla mutane 5 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a Somaliya sakamakon fashewar wani bam da aka dana a wata mota a wani wurin shan kahawa

Rahotonni da suke fitowa da dumi-duminsu daga kasar Somaliya suna bayyana cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a wani wurin sha kahawa mai cike da jama’a a birnin Mogadishu babban birnin kasar Somaliya a yau Litinin, inda nan take mutane 5 suka rasa rayukansu yayin da wasu mutane 20 suka jikkata.

Shafukan yanar gizo na cikin gida sun bayyana cewa: Fashewar bom din ta faru ne a lokacin da mutane suka fara taruwa a shagon shan kahawar ce don kallon wasan kwallon kafa na Yurob 2024 da ke tafe tsakanin kasashen Spain da Ingila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments