Hare-Haren HKI Kan Wata Makaranta A Gaza Ya Kashe Mutane 46 Daga Ciki Harda Yara Kanana

Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46

Wasu hare-haren da HKI ta kai kan gaza sun fada kan wata makaranta wacce aka maida ita wurin kwana, inda ya zuwa yanzu mutane 46 suka yi shahada a yayinda wasu 31 suka ji rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da yara kanana.

Tashar talabijan ta Presstv ta bayyana cewa zana ganin yara suna gudu a cikin wuta suna kokaron kubutar da kansu. Labarin ya kara da cewa makarantar tana unguwar Daraj na birnin Gaza, mai suna Fahmi al-Jarjawi. Majiyar kungiyar kula da fararen hula a gazar ta bayyana cewa yahudawan kai hare haren a safiyar yau litinin a lokacinda suke barci.

Labarin ya kara da cewa a cikin wadanda yahudawan suka kashe a Gaza, akwai Mohammad Al-kasih shugaban bangaren yansandan bincike na arewacin Gaza da Matarsa da yayansa.

Wata majiyar Palasdinawa ta bayyana cewa kafin hari a kan makarantar yahudawan sun kai hare kan wani gida a unguwar Thawra da birnin Gaza.

Manufar yahudawan dai shi ne mamayar dukkan gaza da kuma korar Falasdinawa daga yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted