Jiragen yakin HKI sun jefa makamai masu karfi a kan garin Tartus na yammacin kasar Siriya, wanda ya yi kama da makamai nukliyan da Amurka ta yi amfani da su a kan birnin Hiroshima na kasar Japan a kasarshen yakin duniya na 2.
Tashar talabjin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa hare-haren HKI a kan garin Tartus a daren jiya Lahadi ya girgiza birnin ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Labarin ya kara da cewa hare-haren na Tartus sune mafi muni tun lokacinda sojojin HK suka fara kai hare hare kan kayakin yaki da kuma rumbunan ajiyar makamai na kasar ta Siriya bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad.
Har’ila yau kungiyar ‘kare hakkin bil’adama ta kasar Siriya” ta ce sojojin yahudawan sun kai hare hare kan makamai masu linzami a garin Tartus inda suka lalatasu, sannan sun wargaza kayakin tsaron sararin samaniyar kasar da suke garin. Labarin ya kara da cewa karfim makaman da suka jefa, ya girgiza kasar garin har zuwa karfin ma’aunin richter 3. Inji kungiyar.