Hare Haren Hizbullah Kan Sansanonin Sojojin HKI A Arewacin Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai hare hare kan sansanonin sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye tare da amfani

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai hare hare kan sansanonin sojojin HKI a arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye tare da amfani da makaman ‘Drones’ ko jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kuma na kunan bakin wake.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto bayanan da kungiyar ta fitar a jiya talata ne cewa, ta kai wadan nan hare hare ne saboda goyon bayan falasdinawa wadanda sojojin HKI suke yiwa kisan kiyashi a Gaza, da kuma hare haren da sojojin HKI suka kai yankin Bikaa na kudancin kasar Lebanon.

Bayanan sun kara da cewa da farko sun cilla makman ‘Drones’ ne kan sansanin sojojin HKI mail amba 91 a yankin Naahel-Ghairshum. Inda makaman suka halaka wasu daga cikin sojojin yahudawan sannan wasu kuma suka ji Rauni. Har’ila yau makaman sun wargaza sansanin sun kuma kona shi.

Sannan a sansanin sojoji na ‘Bayad Balid’ kuma sun yi luguden wuta a kansa da makaman Roka. Banda Haka a ‘Birke Risho’ ma ta cilla makaman roka a sansanon sojojin yahudawan dake can. Tun bayan fara yakin Tufanul Aksa a zirin gaza a ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata ne dakarun na Hizbullah suke barin wauta a arewacin HKI wanda ya tilstawa dubban daruruwan yahudawan da suke yankin suka kaurace masa.

Sannan kungiyar ta sha Alwashin zata ci gana tallafawa Falasdina kan HKI har zuwa lokacinda da dakatar da wuta a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments