Dakarun ‘yan tawayen Sudan na kungiyar Rapid Support Forces sun kai hare-hare da suka janyo mutuwar mutane da dama a garin El- Fasher
Hare-haren Dakarun kai dauki gaggawa na Rapid Support Forces kan garin El-Fasher na Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 38 tare da jikkata wasu 280 na daban a tsawon kwanaki biyu da suka gabata. Yayin da Amurka ta yi gargadin cewa birnin na El-Fasher yana gab da samun bullar wani kazamin kisan kiyashi, don haka ta yi kira ga bangarorin da ke dauke da makamai da su dakatar da ta’addanci kan fararen hula tare da kare rayukansu.
A rahoton da ma’aikatar lafiya ta yankin Darfur ta fitar yana nuni da cewa: Sakamakon wasu sabbin hare-hare da mayakan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai kan birnin El Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa da ke yammacin kasar Sudan, mutane kimanin 50 ne suka mutu, yayin da wasu akalla 280 na daban suka jikkata.