wani babban jami’I a kungiyar gwagwarmaya ta hamas ya fadi cewa kungiyar ta cika dukkan nauyin da ya rataya a wuyanta a yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakaninta da yahudawan sahyuniya bayan da ta mika gawar karshe na mutanen da ta kama .
Husam Badran ya bayyana a hukumance cewa mika mutum na karshe da ta kama a gaza ya rufe bakin duk wata dama da prime minister isra’ila Banjemen Natanyaho yake fakewa da ita wajen jinkirin aiwatar da yarjejeniyar.
har ila yau yayi kira ga masu shiga tsakani da su kara kaimi wajen matsin lamba ga Isra’ila ta yi aiki da dukkan sharuddan a yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu, Kuma yayi barazanarr cewa ci gaba da keta yarjejeniyar da Isra’ila ke yi zai jefata cikin hatsarin ci gaba da wanzuwa.
yace dole ne gwamnatin sahyuniya ta janye daga yankin Gaza kuma ta bada damar shigar da kayayyakin agaji a yankin, kuma a bude mashigar rafah daga dukkan bangarorin biyu, yace isra’ila na ci gaba da keta yarjejeniyar ba kakkautawa kuma yana jawo mutuwar falasdinawa fararen hula da yawa kuma yana kara tsananta matsalar da ake ciki a yankin