Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya

Kungiyar Hamas wace take iko da yankin gaza ta bada sanarwan cewa, zata mika makamanta ne kawai ga gwamnatin Falasdinawa wacce take da cikekken iko

Kungiyar Hamas wace take iko da yankin gaza ta bada sanarwan cewa, zata mika makamanta ne kawai ga gwamnatin Falasdinawa wacce take da cikekken iko a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, idan yahudawan sun kawo karshen mamayar da sukewa kasar.

Shafin labarai na yanar Gizo ArabNews ya nakalto shugaban kungiyar Khalilul Hauua yana fadar haka ya kuma kara da cewa ; idan HKI ta kawo karshen mamayar da takewa kasar Falasdinu gaba dayanta, Hamas zata mika makamanta ga gwamnatin Falasdinawa wacce al-ummar Falasdinu ta zaba.

Ya ce ; Samuwar Makamammu na da dangantaka da mamaye, don haka a duk lokacinda HKI ta kawo karshen mamayar kasar Falasdinu (daga teku zuwa ) a lokacin kungiyar Hamas zata mika makamanta ga gwamnatin Falasdinawa wacce falasdinawa suka zaba don gudanar da kasar.

A wani bangaren kuma Al-Hayya ya ce, Hamas ta amince da dakarun tabbatar da zaman lafiya idan aikinsu shi ne kiyaye kan iyakoki Falasdinu da kasashe makobta, amma idan aikinsa shi ne kwace damarar kungiyar Hamas ne to basa maraba da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted