Shugaban tawagar masu tattaunawar tsagaita wuta na kungiyar Hamas a Gaza ya bayyana cewa duk wata yarjeniya tare da samuwar sojojin HKI a Gaza ba karbebbe Bane.
Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS na kasar Iran yanakalto Khalilul Hay shugaban tawagar tattaunawa tsagaita wuta a Gaza, yana fadar haka ya kuma kara da cewa: Idan shugaba Biden yana bukatar a tsagaita wuta a Gaza, to dole ne ya tursasawa Natanyahu ya amince da abinda ya amince tun farko na janye sojojin sa daga Gaza.
Khalil ya kara da cewa bama bukatar wata sabuwar tattaunawa wacce zata maidamu daga inda muka fara. Tattaunawa ta kare kuma dole ne gwamnatin Natanyahu ta amince da janye sojojinsa gaba daya daga gaza kafin a yi maganar musayar fursononi, ko wani abu daban.
A ranar 15-16 ga watan Augusta na shekarar da muke ciki ne aka gudanar da taron tattauna batun tsagaita wuta a gaza, a birnin Doha na kasar Qatar, wanda kuma ya sami halattan wakilai daga kungiyar Hamas, masar, Qatar, Amurka da kuma HKI, amma dagewar firai ministan HKI Benyamin Natanyahu na ci gaba da kissan Falasdinawa a gaza ne ya hana yarjeniyar kankama.