Hamas Ta Yi Maraba Da Matakin Armeniya Na Amincewa Da Falasdinu A Matsayin Kasa

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin Jamhuriyar Armeniya na amincewa da Falasdinu a matsayin Kasa A hukumance. Hamas ta dauki matakin

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin Jamhuriyar Armeniya na amincewa da Falasdinu a matsayin Kasa A hukumance.

Hamas ta dauki matakin na Armeniya a matsayin wani muhimmin mataki na shafe fagen kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu mai cikakken iko da Kudus a matsayin babban birninta.”

Hamas ta sake sabunta kiranta na “kasashe a duniya da su dauki irin wadannan matakai na goyon bayan gwagwarmayar da Falasdinawa ke yi na samun kasarsu da kuma kawo karshen ‘yan mamaya.

A jiya Juma’a ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Armeniya ta sanar da amincewa da kasar Falasdinu.

Sanarwar ta ce, “Domin jaddada kokarinta na tabbatar da bin dokar kasa-da-kasa, da daidaito, da ‘yancin-kai da zaman lumana tsakanin mutane, Jumhuriyar Armenia ta amince da Ƙasar Falasdinu”.

Ma’aikatar ta ce a baya kasar Armenia ta goyi bayan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ke kiran a tsagaita wuta nan-take a yakin Gaza, inda Isra’ila ta kashe Falasdinawa 37,000 tun Oktoban bara.

Armeni ta kuma soki hare-haren Isra’ila kan ababen more rayuwa na farar hula, da kuma zaluntarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments