Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Matsayin Amurka Na Goyon Bayan Haramta Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa Ta UN

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA)

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai.

A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka ta yi a baya-bayan nan a gaban kotun kasa da kasa domin ganin an yi watsi da zarge-zargen da ake yi kan aikata laifuka yaki kan ‘yan sahayoniyya, ya yi daidai da matsayar gwamnatin mamayar Isra’ila, da ke da nufin gurgunta rawar da hukumar UNRWA ke takawa wajen yi wa ‘yan gudun hijirar Falasdinu hidima, da kuma tsaurara matakan tsaro a zirin Gaza, yayin da ake ci gaba da aiwatar da “laifi na kakaba masifar yunwa” kan fararen hula.

Kungiyar Hamas ta ce zargin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi wa hukumar UNRWA ta Majalisar Dinkin Duniya “karya ce karara” da nufin kawar da rawar da hukumar ta UNRWA ke takawa da kuma kawo karshen ayyukan jin kai da ta ke yi musamman kan batun ‘yan gudun hijirar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments