Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas

Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji.

“Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza.

Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.”

Sanarwar ta karyata ikirarin CENTCOM cewa “kusan kasashe 40 da kungiyoyin kasa da kasa suna aiki a Gaza,” yana mai jaddada cewa ainihin adadin kungiyoyin da ke ba da agajin jin kai bai wuce 22 ba, “yawancinsu suna fama da cikas da kuntatawa saboda matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ta sanya.”

Haka kuma ta soki shiru da CENTCOM ta yi game da laifuka da cin zarafi da Isra’ila ke yi a kullum tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba.

“Shirun da rundunar sojin Amurka ta yi a gaban wadannan laifukan na yau da kullum, yayin da take aiki don yada labaran da ba su da tushe game da rundunar ‘yan sandan Falasdinu, ya nuna cikakken son kai ga mamayar Isra’ila da kuma rashin sahihancinta a matsayin wacce ya kamata ta kasance mai shiga tsakani,” in ji sanarwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments